Leicester : Za mu farfado a Premier

Leicester na ganin nasarar za ta karfafa musu guiwa

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Leicester ba ta ci wasa ko daya ba na Premier a wannan shekarar ta 2017

Leicester City za ta iya amfani da nasarar da ta samu da ci 3-1 a wasanta da Derby County, na cin kofin FA, wajen farfadowa a gasar Premier, in ji dan wasanta Andy King.

Dan wasan tsakiya na zakarun Premier Andy King shi ne ya fadi haka bayan sun doke Derby 3-1 a maimaicin wasan na zagaye na hudu ranar Laraba .

Dan wasan na Wales ya ce, irin yadda suka yi wasan na ranar Laraba, ya nuna karfin guiwar da suke da shi, wanda za su iya fita daga hlin da suke ciki a Premier.

Maki daya ne tsakanin kungiyar ta Leicester da rukunin faduwa daga gasar Premier, inda take matsayi na 16 da maki 21, a wasa 24.

Nasarar ita ce ta farko da Leicester City ta samu a wannan shekara ta 2017, wadda kuma ta ba ta damar zuwa zagayen 'yan 16.

Wasan na ranar Laraba dai maimaici ne na zagaye na hudu, bayan da a karon farko suka tashi canjaras 2-2.

A karawar kungiyoyin sun kammala minti 90 na wasan ne da kunnen doki 1-1, abin da ya sa aka tsawaita shi har zuwa lokacin raba-gardama na karin ,inti 30.

A minti na 46 ne da fara wasa King ya ci wa Leicester kwallonta, kafin Camara ya farke a minti na 61.

Minti hudu da shiga lokacin raba-gardamar sai Ndidi ya ci wa Zakarun na Premier kwallo ta biyu.

A minti na 114 na wasan ne kuma sai Gray ya kara ci wa masu masaukin bakin kwallo ta uku.

Yanzu dai Leicester za ta fafata da One Millwall a zagayen 'yan 16 a ranar Asabar 18, ga watan Fabrairun nan, a filin wasa na The Den, na Millwall.