Har yanzu Arsenal ba ta fitar da rai da kofin Premier ba - Wenger

Arsene Wenger a ciki 'yan kallo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Arsene Wenger na hukuncin hana shi shiga fili na wasa hudu

Arsene Wenger ya ce dole ne Arsenal ta yi imani cewa har yanzu za ta iya daukar kofin Premier a bana duk da tazarar maki 12 da ke tsakaninta da Chelsea ta daya.

Wenger ya ce: ''Ni dai ban karaya ba, ko da ku ('yan jarida) kuna ganin, ba sauran wata dama, ni ban yanke kauna ba, ba ma wannan tunanin.''

Kocin, dan Faransa ya kara da cewa, idan har za a ce ba su da wata dama, to sai a ce kowa ma ba shi da sauran dama, domin kowa na ciki.

Maki biyar ne kawai tsakanin ta biyu a tebur, Tottenham da Manchester United ta shida.

Kocin ya ce Chelsea ta samu dama ne domin, ba sa cikin gasar kofin Turai, ba sa wasan tsakiyar mako, wanda wannan ya kara musu karfi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wasu magoya bayan Arsenal na son Arsene Wenger ya bar kungiyar haka

Arsenal wadda rabonta da daukar kofin Premier tun 2004, ta yo kasa zuwa matsayi na hudu bayan da ta sha kashi 3-1, a gidan Chelsea ranar Asabar da ta wuce.

A ranar Asabar Arsenal din za ta karbi bakuncin Hull City (karfe 1:30 na rana agogon Najeriya), bayan ta yi rashin nasara a wasanta hudu daga cikin tara na Premier, na karshen nan.

Arsenal ta sha kashi a gidan Chelsean ne, kwana hudu bayan Watford ta doke su 2-1 a gida, abin da ya sa har wasu magoya bayan kungiyar suke kira da kocin ya ajiye aiki.