Cheick Tiote ya koma China da wasa

Cheick Tiote a wani wasa na Newcastle

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dan wasan na Ivory Coast, Cheick Tiote, ya yi wa Newcastle wasa 156 a zamansa da kungiyar

Dan wasan tsakiya na Newcastle United, Cheick Tiote, ya koma Beijing Enterprises Group FC da ke rukuni na biyu a China, kan kudin da ba a bayyana ba.

Dan wasan na Ivory Coast ya yi wa Newcastle wasa 139, tun da ya koma kungiyar a watan Agusta na 2010 daga FC Twente ta Holland.

Sai dai dan wasan mai shekara 30 sau uku kawai ya yi wa Newcastle wasa a kakar bana.

Tiote yana daga cikin tawagar Ivory Coast da ta dauki kofin kasashen Afirka na shekarar 2015.