'Griezmann ba zai je Man Untd ba'

Antoine Griezmann

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Griezmann ba zai je kungiyar da ba za ta gasar kofin Zakarun Turai ba

Idan dai har Man United ba ta samu damar zuwa gasar kofin Zakarun Turai ba, ba ta yadda Antoine Griezmann na Atletico Madrid zai koma kungiyar, kuma ko ta samu dama, da wuya ya je.

Dan jarida kuma masani kan harkokin wasan kwallon kafar Turai Andy Brassell ne ya bayyana haka a wata hira da BBC.

Brassel na magana ne kan wasu rahotanni da ke cewa Manchester United na tattaunawa kan sayen dan wasan na Faransa.

Dan jaridar ya ce bayajin ciniki ne mai sauki, domin akwai abubuwa da dama da za a yi la'akari da su a kn barin dan wasan kungiyarsa a yanzu.

Ya ce bayan cewa wasan gasar ZakarunTurai abu ne mai muhimmancin gaske a wurin Griezmann, akwai kuma wasu abubuwa da za su iya hana zuwan dan wasan United.

Babba daga cikinsu shi ne yadda dan wasan zai iya kasancewa tare da Paul Pogba, domin abu ne mai wuya a iya hada su wasa tare.

Brassell ya ce shi kansa Griezmann, ya kwana da sanin yadda ake faman ganin yadda za a iya hada su wasa tare a tawagar kasar Faransa.

Ya ce duk tsarin da aka yi idan ya yi wa Griezmann daidai, sai a ga bai yi wa Pogba daidai ba.

Haka kuma idan tsari ya dace da Pogba, sai a ga bai dace da Griezmann ba.

Saboda haka yana ganin idan Man United ta sayo Griezmann kamar za ta ajiye Pogba kenan, wanda shi ne dan wasanta mafi tsada, kuma da wuya hakan ta tabbata.