Kofin Duniya: Uefa za ta nemi gurbi 16

"yan wasan Jamus na murnar daukar Kofin Duniya na 2014 a Brazil

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jamus ta dauki Kofin Duniya a karo na hudu, inda ta doke Argentina a Brazil a 2014

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta ce za ta bukaci a ba wa kasashenta gurbi 16 a gasar kofin duniya ta 2026 da za a fadada zuwa kasashe 48.

Haka kuma Uefan ta ce za ta nemi a rarraba kasashen Turai da suka samu gurbin zuwa gasar daban-daban, ka da a hada wata kasa da takwararta ta Turai wuri daya a matakin farko.

A sabon tsarin gasar za a fara da rukuni-rukuni guda 16, da ke dauke da kungiyoyi uku-uku, inda za a yi wasannin neman zuwa mataki na gaba har zuwa matakin sili-daya-kwale.

Kasashen Turai 13 ne suka samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya na 2014 da aka yi a Brazil, wadda Jamus ta dauki kofin.

Shugaban hukumar ta Uefa Aleksander Ceferin ya ce dukkanin wadannan bukatau ne da za su yi wu, kuma burinsa shi ne kowace kasa ta Turai ta tsallke tun daga zagayen farko.

Ceferin yana maganar ne a wurin taron kwamitin zartarwa na hukumar ta kwallon kafar Turai a Nyon, Switzerland.

A watan Mayu ne Fifa za ta ware wa kowace nahiya kasonta na gurbin gasar cin kofin duniyar na sabon tsarin.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Gianni Infantino ya ce fadada gasar abu ne da ya dace da karni na 21

A wurin babban taron Fifa ne kasashe suka amince da fadada gasar ta kofin duniya kamar yadda shugabanta Gianni Infantino ya yi alkawari a yakin neman zabensa.

Wasannin gasar za su karu daga 64 zuwa 80, amma kamar da kasashen da suka yi nasara a karshe za su yi wasanni bakwai ne kawai, inda za a kammala gasar cikin kwana 32.