Ba zan sake jin ni gwani ba ne-Woods

Asalin hoton, Getty Images
Babbar gasar karshe da Tiger Woods ya ci ita ce ta US Open a 2008
Tsohon zakaran wasan kwallon Golf na duniya, Tiger Woods, ya ce ba zai sake jin cewa shi gwani-na-gwanaye ne ba, saboda irin raunukan da yai fama da su a lokacin wasansa.
A watan nan na Fabrairu ne Tiger Woods mai shekara 41, wanda sau 14 yana zama na daya a duniya ta manyan kofunan da ya dauka, ya fice daga gasar Dubai Desert Classic, tun kafin zagaye na biyu saboda ciwon baya.
A watan Disamba ne daman ya dawo fagen wasan Golf din bayan an yi masa tiyatar ciwon baya sau biyu.
Woods bai ci wata gasa ba tun shekara ta 2013, kuma rabonsa da cin wata babbar gasa tun shekara ta 2008.
Yana sa ran zai shiga gasar gwanaye da za a yi a birnin Agusta daga ranakun 6 zuwa 9 na Afrilu.
Tsohon zakaran kwallon golf din na duniya, ya ce, yanzu al'amaru sun sauya, zamaninsu ya fara nisa, amma duk haka idan har zai shiga gasa to burinsa shi ne ya yi nasara.