Nile Ranger ya dawo fagen wasa

Nile Ranger
Bayanan hoto,

Nile Ranger ya ci kwallaye uku a wasanni 15 da ya yi tun bayan da ya koma wasa Southend a watan Agusta

Dan wasan gaba na kungiyar Southend United Nile Ranger, ya dawo fagen wasa bayan da hukumar kwallon kafa ta Ingila FA, ta kammala bincike a kansa.

An dakatar da Ranger ne daga buga gasar League One a ranar 12 ga watan Janairu bayan ya karya dokar da'a, inda aka hana shi yin wasa har sai an kammala binciken.

A ranar Alhamis ne FA ta wanke dan wasan mai shekara 25 tare da ba shi damar komawa fagen wasa, bayan kwanaki 28 da dakatar da shi da hukumar ta yi.

Akwai yiwuwar zai bugawa kungiyarsa ta Southend a ranar Asabar, inda za ta kara da Millwall.

A farkon watan Janairu ne dan wasan ya amsa laifin cewa ya yi wata zambar kudi a banki ta intanet, amma an yi amanna dakatarwar tasa ba ta da alaka da wannan.