'Rashin gwajin kwaya a La Liga na damun mu'

WADA Hakkin mallakar hoto PA

Hukumar hana amfani da kwayoyin kara kuzari ta duniya WADA, ta ce rashin yin gwajin kwayoyin kara kuzari a harkar kwallon kafar Spaniya abin tashin hankali ne.

A watan Maris din shekarar 2016 ne WADA ta ayyana hukumar hana amfani da shan kwayoyin kara kuzari ta Sipaniya AEPSAD, a matsayin mara bin doka.

A wata sanarwa da ta fitar, WADA ta ce, "Hakan zai dakile kokarin da ake na tsaftace harkar wasanni a duniya."

WADA ta bayyana fatanta na cewar hukumomin kwallon kafar duniya da ta Turai za su dauki wani matakin wucin gadi kan lamarin, amma dai ba a kai ga cimma wata yarjejeniya ba.

Bayan wani mataki da aka dauka a kan AEPSAD, an dakatar da wani dakin gwaje-gwaje na WADA da ke Madrid a watan Yuni, aka kuma hana shi yin duk wani gwajin fitsari ko jini da ya danganci shan kwayoyi.

WADA ta ce, "Rashin gudanar da gwaji a kasar da ke kan gaba wajen wasan kwallon kafa na kungiyoyi fiye da kusan shekara daya, babban abin daga hankali ne."