Burnley ta rike Chelsea 1-1

Kwallon da Brady ya ci Thibaut Courtois Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A karon farko an ci Thibaut Courtois da bugun tazara a gasar Premier

Burnley ta rike Chelsea da kunnen doki 1-1, a wasan mako na 25, amma duk da haka jagorar ta Premier ta kara tazara da maki 10 a teburin gasar.

Pedro ne ya fara ci wa jagorar Premier kwallo a minti na 27 da shiga fili.

Masu masaukin bakin, Burnley, sun rama kwallon ne ta hannun dan wasansu mafi tsada da suka sayo a watan Janairu Brady daga Norwich, ana minti 27 da wasa.

Kwallon da Brady din ya ci da bugun tazara, a wasansa na farko a Burnley, ita ce ta farko da aka taba cin mai tsaron ragar Chelsea Courtois, tun da ya zo gasar Premier.

Da wannan sakamako har yanzu Chelsea ce ta daya a tebur da maki 60, a wasa 25, yayin da Tottenham ke bi mata baya da maki 50.

Burnley kuwa ta dago sama inda ta zama ta 12 da maki 30 daidai da Southampton ta 11, amma da bambancin yawan kwallo.

Southampton tana da bashin kwallo uku (-3), Yayin da Burnley take da bashin kwallo tara (-9).

Ita ma Watford sakamakon wasan ya shafe ta, domin ta yo kasa, zuwa matsayi na 13, amma ita ma da maki 30, sai bashin kwallo 13.