Ban ce zan bar Arsenal ba - Wenger

Arsene Wenger a lokacin da yake kallon wasansu da Hull City a cikin 'yan kallo Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Wenger wanda ya kalli wasansu da Hull a cikin 'yan kallo, ya fara kocin Arsenal tun Oktoban 1996

Arsene Wenger ya musanta cewa ya gaya wa Ian Wright cewa zai yi ritaya daga aikin kociyan Arsenal a karshen kakar bana.

A ranar Juma'a ne Ian wanda tsohon dan wasan Arsenal ne, a wani shirin BBC ya bayyana cewa, ya ga alama Wenger ya gaji.

Kuma kocin ya nuna masa alamar cewa a karshen kakar da ake ciki zai kawo karshen aikinsa a Arsenal.

Sai dai Wenger a martanin da ya mayar game da wannan magana ta Ian Wright, ya ce, lalle sun yi wani zama na cin abincin dare tare.

Amma kuma ba su biyu ba ne kawai a lokacin.

Sannan Wenger ya ce: ''Na gode sosai da kake son na huta, amma ban shirya ba tukuna.''

Ya kara da cewa: ''Lalle zai ga alama na gaji, saboda ina tashi da safe ne da wuri.''

Tun a watan Satumba na 1996 ne Wnger mai shekara 67 ya kama aikin horar da Arsenal.

Duk da martanin na Wenger, Ian Wright, wanda ya yi wasan kaka biyu tsakanin 1996 da 1998 a karkashin Wenger, ya jaddada cewa shi kam ya yi amanna, Wenger zai tafi.

Ian Wright mai shekara 53, ya ce, sun yi zama ne da za a ce na tambaya da amsa da kocin, kuma daga abin da ya fahimta shi dai yana ganin Wenger zai yi ritaya a karshen kakar bana.

Wenger shi ne kocin da ya fi dadewa a gasar Premier, kuma kwantiraginsa za ta kare a karshen kakar nan.

Kocin dan kasar Faransa ya dauki kofin Premier na karshe ne tun 2004, kuma yana shan matsin lamba, sakamakon doke su da Watford da kuma Chelsea suka yi.

Amma kuma bayan da Arsenal din ta doke Hull City 2-0, an ruwaito shi yana cewa: ''Ina mayar da hankali ne akan abin da yake da muhimmanci:

Cin wasa da kuma shirya 'yan wasan su yi kokari. Sauran kuwa, abu ne da ba ni da iko a kai.''