Aleix Vidal ba zai sake wasa ba bana

LOkacin da Aleix Vidal ya ji rauni

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An yi waje da Aleix Vidal lokacin Barcelona na gaba da ci 6-0

Dan wasan baya na Barcelona Aleix Vidal ba zai sake buga wasa ba a bana sakamakon targaden da ya yi a wuyan hannunsa a lokacin wasan La Liga da suka ci Alaves 6-0 ranar Asabar.

An dai yi waje ne da dan wasan na baya mai shekara 27 ne, bayan da ya ji raunin a sakamakon haduwar da suka yi da dan wasan Alaves Theo Hernandez, a minti na 85 na wasan na La Liga na ranar Asabar.

A sanarwar da Barcelona ta fitar ta ce, Vidal wanda ya koma kungiyar daga Sevilla a 2015, zai yi jinyar wata biyar.

Dan wasan ya kasance cikin wadanda koci Luis Enrique, yake sa wa akai akai, inda ya ci wa Barcelona kwallaye a wasanninta da Las Palmas da Athletic Bilbao, a shekarar nan.

Raunin nasa na daya daga cikin biyu mafiya muni da 'yan wasa suka ji a wasannin La Liga ranar Asabar.

Bayan nasa, sai na dan wasan Osasuna na baya Tano Bonnin, wanda ya karye a kafa, kafin a tafi hutun rabin lokaci a wasan da Real Madrid ta ci su a gida 3-1.