Kila na daina buga fanareti - Dzeko

Edin Dzeko a lokacin da zai buga fanaretin Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Edin Dzeko ya wanke kansa da ya ci kwallonsa ta 18 a gasar ta Serie A, a wasan bayan ya barar da fanaretin tun da farko

Edin Dzeko ya ce zai daina buga fanareti bayan da ya barar da ta biyu a wasanni biyar na gasar Serie A ta Italiya, a kungiyar Roma, wadda ta doke Crotone 2-0 ta zama ta biyu a tebur.

Dzeko, tsohon dan wasan Manchester City, wanda shi ne kan gaba wajen yawan cin kwallo a gasar ta Italiya a bana, ya barar da fanaretin ne, inda ya buga kwallon gefe, a lokacin ba inda aka ci a wasan.

Sai dai dan wasan na kasar Bosnia-Herzegovina ya kasance dodon-raga a Roma, inda ya wanke kansa da ya ci kwallonsa ta 18 a gasar ta Serie A, ana sauran minti 13 a tashi daga wasan.

Daman tun kafin ya ci Nainggolan ne ya fara ci wa Roman ana minti 40 da wasa.

Bayan da ya zubar da fanaretin ne Dzekon ya ce, nan gaba kila zai bar wa wani ya buga.

Ya ce a karshe dai ya ci kwallonsa, wanda wannan shi ne mafi muhimmanci. Ita fanareti daman ba ta da tabbas.

Nasarar ta sa Roma ta sake komawa saman Napoli, wadda ta doke Genoa 2-0 ranar Juma'a, amma duka kungiyoyin biyu suna bin Juventus ne ta daya a baya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hoton faanaretin da Dzeko ya barar a gidan Udinese a watan Janairu ya karade shafukan intanet

Juventus ta daya tana da maki 57 a wasa 23, yayin da Roma ta biyu take da maki 53 a wasa 24, sai kuma Napoli ta uku da maki 51, ita ma a wasa 24.

A ranar Alhamis ne, Roma za ta je Spaniya inda za ta kara da Villareal a wasan karon farko na gasar kofin Europa na rukunin kungiyoyi 32.

Ga sakamakon sauran wasannin na Serie A na Lahadi 12 ga watan Fabrairu 2017:

Inter MIlan 2-0 Empoli

Palermo 1-3 Atalanta

Sassuolo 1-3 Chievo

Torino 5-3 Pescara

Sampdoria 3-1 Bologna

Cagliari da Juventus (ana wasan)