Swansea ta kara jefa Leicester cikin hadari da 2-0

Daya daga cikin kwallaye biyun da Swansea ta jefa ragar Leicester Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Swansea ta farfado daga kasan tebur ta zama ta 15 tun lokacin da Paul Clement ya zama sabon kocinta ranar 3 ga watan Janairu

Zakarun Premier Leicester City sun kara shiga hadarin faduwa daga gasar Premier bayan da Swansea a gidanta ta doke su da ci 2-0.

Mawson ne ya fara cin bakin a minti na 36 da shiga fili,kafin kuma Olsson ya kara ta biyu bayan cikar minti 45 na kashin farko, ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.

Wannan shi ne karo na biyar a jere da Leicester ke shan kashi a gasar ta Premier, abin da ke kara sa kocinsu Claudio Ranieri cikin matsi.

Maki daya ne kawai tsakanin kungiyar da layin faduwa daga gasar ta Premier, kuma ita ce kungiya daya a cikin manyan rukunan wasan kwallon kafa na Ingila da ba ta ci kwallo ko daya ba a gasar da take ciki a wannan shekara ta 2017.

Sun kuma kasance Zakaru na farko da ke rike da kofi, da aka doke su a manyan wasanni biyar a jere, tun bayan Chelsea da aka yi wa haka a watan Maris na 1956.

Da wannan yanzu sun samu kansu a cikin rukunin masu faduwa daga gasar ta Premier mai rintsi, inda bambancin maki biyar ne kawai yake tsakanin kungiyoyi biyar da ke cikin hadarin faduwar.

Ita kuwa Swansea ta yi nasara a wasanta uku daga cikin biyar na Premier, tun lokacin da sabon kocinta Paul Clement ya kama aiki ranar uku ga watan Janairu.

Wannan kokari nasa ne ya sa ya ceto kungiyar daga kasan tebur, kuma ya fitar da ita daga cikin kungiyoyi uku da ke cikin hadarin faduwa daga gasar ta Premier, kuma da hakan tsohon kocin na kungiyar Derby County ya samu lambar yabo ta wata-wata ta kocin Premier da ya fi bajinta.

Nasarar ta wannan wasa wadda ita ce ta hudu a wasa shida karkashin Clement ta sa Swansea ta zama ta 15 yanzu, maki hudu tsakaninta da masu faduwa daga gasar Premier.

A lokacin da Leicester za ta yi wasanta na Premier na gaba, inda za ta karbi bakuncin Liverpool ranar Litinin 27 ga watan Fabrairu (9:00 da dare agogon Najeriya), za ta iya kasancewa ta karshen tebur a lokacin, domin duk kungiyoyi uku da ke kasanta za su yi wasansu kafin nata.

Wasan Swansea na gaba shi ne wanda za ta je wa jagorar Premier Chelsea ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu (4:00 na yamma agogon Najeriya).