Bale ya dawo atisaye da Real Madrid.

Gareth Bale dan wasan yankin Wales Hakkin mallakar hoto Huw Evans picture agency
Image caption Gareth Bale ya ci wa Wales kwallo 26

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce yana sa ran Gareth Bale ya dawo buga wasa nan da wata daya, bayan da ya dawo atisaye daga jinyar da ya yi.

Hakan na nufin Bale dan yankin Wales zai iya buga wasan neman zuwa gasar cin Kofin Duniya da Wales za ta yi da Jamhuriyar Ireland ranar 24 ga watan Maris.

Rabon dan wasan mai shekara 27 da taka leda tun watan Nuwamba, bayan da aka yi masa tiyata ta ciwon da ya ji a gara, a lokacin wasansu na cin Kofin Zakarun Turai da kungiyar Sporting.

A wani sako da ya rubuta a shafinsa na Twitter Bale ya ce: ''Ranata ta farko ta atisaye da 'yan wasan kungiyar, na zaku in dawo fagen wasa.''

Sai dai Zidane bai bayyana ainahin ranar da Bale zai dawo wasa ba, amma dai yana sa ran dan wasan zai buga wasan Madrid na biyu na cin Kofin Zakarun Turai da za ta yi da Napoli ranar 7 ga watan Maris.

Tuni kocin Wales Chris Coleman ya sa ran dan wasan zai kasance da tawagar yankin na Wales a lokacin wasansu na neman gurbin gasar cin Kofin Duniya .