Dan wasan Swansea City Nathan Dyer ya tafi jinya

Dan wasan Swansea City Nathan Dyer Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan Swansea City Nathan Dyer ya tafi jinya

Dan wasan gefe na Swansea City Nathan Dyer ya tafi jinyar raunin da ya ji a cinya wadda za ta kai shi har karshen kakar bana ba tare da ya sake wasa ba.

Dan wasan mai shekara 29 ya ji raunin ne bayan minti bakwai kawai da fara wasan da suka doke masu rike da kofin Premier Leicester City 2-0 ranar Lahadi.

Nan da wani dan lokaci ne za a yi wa Dyer wanda ya dauki kofin Premier bara lokacin yan zaman aro a Leicester tiyata.

Tsohon dan wasan na Southampton ya yi wasa sau biyar tun lokacin da aka nada Paul Clement a matsayin sabon kocin Swansea a watan da ya wuce.

Labarai masu alaka