Damben Boksin :Pacquiao ya nemi mabiyansa na Twitter su zaba masa abokin karawa

boxing

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Manny Pacquiao

Zakaran damben boksin na ajin matsakaita nauyi, mai rike da kambin duniya na hukumar WBO Manny Pacquiao ya bukaci mabiyansa na shafin Twitter da su zaba masa abokin karawarsa na gaba.

'Yan dambe hudu da ake sa ran za su kara da Pacquiao. Sun hada da 'yan Birtaniya biyu wato Amir Khan da Kell Brook, sai kuma Jeff Horn dan Australia da kuma Ba'amurke Terence Crawford.

Pacquiao ya ce damben da zai yi na gaba wanda ya ci kambinsa a watan Nuwamba, zai kasance ne a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Dan damben mai shekara 38, dan kasar Phillipines, wanda zakaran duniya ne a ajin nauyi daban-daban har shida, a watan Afrilu ya yi ritaya daga boksin, amma kuma ya sake dawowa fagen damben, ya doke Jessie Vargas.

A watan Disamba ne wakilin Brook, Eddie Hearn ya gaya wa BBC cewa yana tattaunawa a kan karawa da Amir Khan.

Dukkanin 'yan damben boksin din biyu sun yi rashin nasara a karawarsu, inda Brook ya sha kashi a hannun Gennady Golovkin, shi kuwa Khan Saul 'Canelo' Alvarez ya doke shi.

A shekarar 2015, Khan ya ce an tsara shi zai fuskanci Pacquiao a karawar gaba, amma kuma wai zakaran ba ya son dambatawa da shi.