Zakarun Turai : Tarihin haduwar Dortmund da Benfica

Dan wasan tawagar Jamus da ta dauki Kofin Duniya na 2014, na Dortmund Mario Gotze Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mario Gotze wanda ya ci wa Dortmund kwallo 2 a wasa 16 a bana, ba zai yi wasan ba

Mario Gotze ba ya cikin 'yan wasan da za su buga wa Borussia Dortmund karawarta ta farko ta ranar Talata ta zagayen kungiyoyi 16 ta Kofin Zakarun Turai a gidan Benfica.

Dan wasan na tsakiya mai shekara 24, yana fama ne da ciwon kafa, wanda ya hana shi wasan da Dortmund ta sha mamaki, ta karshe a teburin Bundesligar Jamus Darmstadt ta doke ta 2-1.

Sai dai kyaftin din kungiyar Marcel Schmelzer da Lukasz Piszczek, wadanda ba su buga wasansu da Darmstadt din ba saboda jinya, za su yi wasan na Talata.

Ita kuwa Benfica tana sa ran dan wasanta Eduardo Salvio, zai dawo fili, ya taka leda bayan jinyar da ya yi ta kafa.

Sai dai kuma babu tabbas ko dan wasanta na gaba dan Brazil Jonas, zai yi wasan na Kofin Zakarun Turai, saboda bai halarci atisaye ba ranar Litinin.

Dortmund na fama da matsala tun a watan Disamba, inda ta yi nasara a wasanninta biyu kadai, daga cikin tara zuwa yanzu.

Sai dai sau daya ne kawai aka doke ta a wasannin, wanda shi ne na ranar Asabar a gidan Darmstadt.

To amma kociyan kungiyar ta Jamus Thomas Tuchel yana fatan samun gagarumar nasara a wasan nasu na Portugal, domin samun kwarin guiwa a kakar ta bana.

Tarihin kungiyoyin biyu a Kofin Zakarun Turai:

Borussia Dortmund ta fitar da Benfica a zagayen farko na wasan cin Kofin Zakarun Turai a kakar 1963-64, wadda ita ce haduwar da suka taba yi a baya.

Dortmund ta sha kashi da ci 2-1 a karon farko, amma a haduwa ta biyu a Jamus sai ta doke Benfica da ci 5-0.

A tarihi sau daya kawai Benfica ta yi nasara a wasanninta 15 na Kofin Turai da kungiyoyin Jamus, a haduwarta da Kaiserslautern a watan Nuwamba na 1998, inda ta yi canjasar a guda 5, kuma aka doke ta a tara.

Borussia Dortmund ta yi nasara a dukkanin lokuta hudu da ta je matakin sili-daya-kwale na gasar, kuma ita ke zama ta daya.

Borussia Dortmund ce kungiya daya daga cikin shida, da har yanzu ba a doke ta ba a gasar Kofin Zakarun Turai a bana, inda ta ci wasa 4, kuma ta yi canjaras a 2.

Ta ci wasanta biyu a farkon kakar nan, wanda ta yi da wata kungiyar ta Lisbon, wato Sporting, 2-1 a Portugal da kuma 1-0 a gida, Jamus.

Sai dai kuma, Dortmund din ta sha kashi a wasanta shida daga cikin takwas, da ta yi na matakin sili-daya-kwale na Kofin Zakarun Turan, inda ta ci ragowar biyun.