Lukaku zai tafi jinyar sha-raba

Romelu Lukaku yayin da yake yi wa Everton wasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Romelu Lukaku ya ci wa Everton kwallo 17 a bana

Dan wasan Everton na gaba Romelu Lukaku ba zai samu damar zuwa sansanin atisayen kungiyar ba, wanda za ta yi a Dubai, a wannan makon, saboda zai je ganin likita a Belgium, kan matsalar sha-raba.

Sai dai wasu rahotanni daga kungiyar sun ce ciwon na dan wasan na tawagar Belgium mai shekara 23, ba wani mai tsanani ba ne.

Ana sa ran Lukakun wanda ya ci kwallo 17 a bana, zai dawo har ya yi wasan Premier wanda Everton za ta je gidan Sunderland ranar 25 ga watan nan na Fabrairu.

Saura kwallo daya kacal, dan wasan ya kafa tarihin yawan ci wa kungiyar kwallo irin na Duncan Ferguson, wanda ya ci mata kwallo 60 a gasar Premier.