'Rike Claudio Ranieri kasassaba ce'

Claudio Ranieri na tsaka-mai-wuya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasan Premier biyar kawai Leicester ta ci a kakar bana

Leicester City za su yi babbar kasada idan suka ci gaba da rike kocinyansu Claudio Ranieri, in ji tsohon dan wasan gaba na Blackburn Rovers Chris Sutton.

Sutton ya shaida wa BBC cewa shi bai ga dalilin da zai sa kungiyar ta ci gaba da zama da kociyan ba.

Ya ce, idan da kungiyar ta gama gasar kakar da ta wuce a matsayi na 12, kuma a ce a bana suna cikin wannan halin, da tuni kowa na cewa a sallame shi.

Sutton ya kara da cewa, wasan kwallon kafa, wani shu'umin abu ne, 'yan wasan ba sa taka wa kocin leda sam-sam, saboda haka ina ganin suna cikin tsaka-mai-wuya.

Zakarun na Premier na cikin hadarin faduwa daga gasar Premier, kasancewar mataki daya ne da kuma maki daya kacal tsakaninsu da rukunin masu ficewa daga gasar, bayan doke su da aka yi sau 5 a jere.

A makon da ya gabata ne duk da tsaka-mai-wuyar da kungiyar ke ciki ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce tana tare da kociyan nata, dan Italiya.

Idan 'yan Leicester suka fadi daga gasar Premier, to za su kasance zakarun gasar na farko da suka fadi, tun bayan Manchester City a 1938.

Har yanzu ba su ci ko da wasa daya ba na Premier ko kuma zura kwallo daya ba a gasar tun da shekarar nan ta 2017 ta kama.