Winks ya tsawaita kwantiraginsa a Tottenham

Asalin hoton, Getty Images
Harry Winks ya ci West Ham a cikakken wasansa na farko a Tottenham
Dan wasan Tottenham na tsakiya Harry Winks ya sanya hannu a sabon kwantiragin da zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2022.
Winks, mai shekara 21, ya yi wasa 13 a Premier kuma ya ci West Ham a cikakke wasansa na farko da ya buga wa Tottenham a watan Nuwamba.
Dan wasan na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21, shi ne dan wasa na baya-bayan nan da ya kulla wata yarjejeniya ta tsawon lokaci a kungiyar.
Dan wasan gaba na kungiyar Harry Kane da dan wasansu na tsakiya kuma abokin wasansa a tawagar ta Ingila Dele Alli da kuma golan Faransa Hugo Lloris, dukkaninsu su ma sun sabunta kwantiraginsu a Tottenham din.
Winks wanda ya taso daga karamar kungiyar horar da matasan 'yan wasan Tottenham ya fara wasansa ne a kungiyar a lokacin da ya yi canji a wasansu da Liverpool a watan Agusta.
Haka kuma kungiyar ta sabunta kwantiragin matashin dan wasanta na baya Kyle Walker-Peters, dan shekara 19, wanda bai ma fara yi wa babbar kungiyar wasa ba, har zuwa 2019.