Griezmann ya nesanta kansa da Premier

Antoine Griezmann a karawarsu da Barcelona Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Griezmann ya ci wa Atletico kwallo 16 a wasa 32 kuma ya bayar an ci 8 a bana

Antoine Griezmann ya nesanta kansa da maganar da ake yi ta komawarsa gasar Premier, yana mai cewa yana jin dadin zamansa a Atletico Madrid.

Wasu rahotanni ne ke nuna cewa kungiyoyin Chelsea da Arsenal da Manchester City da kuma Manchester United na zawarcin dan wasan mai shekara 25.

A hirarsa da shafin intanet na Fifa, dan wasan na Faransa, wanda ya samu kyautar zama gwanin dan wasan gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2016, ya kuma yaba wa kocinsu Diego Simeone kan yadda ya ce ya taimaka masa a kwallon kafa.

Dan wasan ya ce: ''Simeone ya sauya ni. Ya koya min abubuwa da dama a wasana, wanda in ba don shi ba, da ban zama daya daga cikin fitattun 'yan wasa ba yau a duniya.

Griezmann ya kuma ce shi a karan kansa yana matukar farin ciki a kungiyarsa, kuma ga shi za su koma sabon filin wasansu, wanda abu ne mai muhimmanci sosai a wurinsu.

A wata hira da ya yi da tashar rediyon Faransa ta RMC, ranar Talata, idan har zai bar Madrid to zai fi son ya tsaya a Spaniya.

Ya ce a Spaniya Barcelona tana da Lionel Messi da Neymar da Kuis Suarez, kuma ba ta yadda zai tafi Real Madrid saboda yana wasa a Atletico.

Kuma ya ce gasar Jamus ba ta ba shi sha'awa, ta Faransa kuwa ba yanzu ba, amma kuma akan gasar Premier ta Ingila, ya ce yana kallon wasanninta, amma yana da tababa akan yanayin rayuwar can.

Ya ce a Ingila akwai ruwan sama da yanayi maras kyau, saboda shi yana son ya ji dadin rayuwarsa a waje, bayan filin wasa.

Griezmann ya kara da cewa, yana sha'awar irin wasan Ingila, domin alkalan wasa suna barin wasan wakana da kyau, sannan 'yan kallo na cika filin wasa kodayaushe.

Amma kuma ya ce gasar La Liga ta Spaniya ta fi dacewa da salon wasansa.

Dan wasan ya koma Atletico Madrid a 2014 a kan kudi fan miliyan 24 daga kungiyar Real Sociedad ita ma ta Spaniya, wadda ta dauke shi tun yana shekara 14.