Askin Asamoah Gyan ya saba wa doka

Asamoah Gyan da salon askinsa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gyan ya je wa Ghana wasan cin kofin kasashen Afirka da aka gama a Gabon

Tsohon dan wasan Sunderland Asamoah Gyan na daga cikin 'yan wasa sama da 40, da aka ayyana cewa gashi ko salon askinsu ya saba wa dokokin hukumar kwallon kafa ta Hadaddiyar Daular Larabawa.

Dan wasan na Ghana mai shekara 31 ya tafi aro ne kungiyar Al Ahli ta Dubai daga Shanghai SIPG ta China.

A bisa wata koyarwar ta addinin Musulunci, an haramta salon askin da za a aske wani sashe kuma a bar wani sashe na kan mutum.

A tsarin wasan kwallon kafar Daular, alkalin wasa ne zai yi hukunci cewa ko salon askin dan wasa ya dace ko kuma ya saba ka'ida.

Alkalan wasa a suna aiwatar da dokar hana 'yan wasa aski maras kan gado ko barin gashi yadda bai dace ba da al'adar Daular, don gudun ka da yara su kwaikwaya.

Sauran kasashe makwabtanta su ma suna aiwatar da irin wannan doka, inda a 2012, alkalin wasa ya umarci golan Saudi Arabia Waleed Abdullah, ya aske gashinsa, wanda ya ce ya saba wa Musulunci, kafin ya bar shi ya yi wa kungiyarsa Al Shabab wasa.

Da farko dai hukumar kwallon kafar ta Hadaddiyar Daular Larabawar tana aika wa kungiyar da dan wasa yake takardar gargadi, da hukunci da yakan kai ga tara, sannan kuma da dakatarwa, idan dan wasa ya ki bin dokar.

A yanzu Gyan na daya daga cikin 'yan wasa 46 da ke matakin farko na takardar gargadi da aka tura wa kungiyoyinsu.