Anceloti ya shawarci Wenger ya jure wa suka

Carlo Ancelotti Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ancelotti ya ce yaba wa Wenger ya kamata a yi kan yadda ya gina Arsenal, amma ba suka ba

Kocin Bayern Munich kungiyar da za ta kara da Arsenal ranar Larabar nan a gasar cin Kofin Zakarun Turai zagayen kungiyoyi 16, karon farko, Carlo Ancelotti ya bayyana irin yadda yake mutunta Arsene Wenger tare da shawartarsa ya jure sukan da ake yi ma sa.

Irin halin rashin kokari da Arsenal take ciki a gasar Premier, ya sa ake ta rade radi kan makomar kociyan dan Faransa a kungiyar, inda har wasu magoya bayanta suke neman da ya tafi.

Kociyan dan italiya, yana ganin maimakon a rika sukan Wenger kamata ya yi ma a yaba masa kan abubuwan da ya yi wa Arsenal, na gina tsari mai karfi da kuma samar da salon wasa mai kyau a kungiyar.

Ancelotti ya kara da cewa, Wenger yana da kwarewar da ya san cewa a aikin koci, suka ba wani sabon abu ba ne, saboda haka ba shi da wata matsala.

Tsohon kociyan na Chelsea yana magana ne kafin wasansu na farko na cin Kofin Zakarun Turai, zagayen kungiyoyi 16, na sili-daya-kwale, a Jamus.

Kasancewar Arsenal tana ta hudu a teburin Premier da tazarar maki 10 tsakaninta da ta daya Chelsea, ana ganin damar da kungiyar ke da ita ta cin wani kofi a bana, tana kan gasar Kofin Zakarun Turai ne da Kofin FA, kawai.

Arsenal na da gagarumin aiki a gabanta na haduwa da Bayern, kungiyar da ta hadu da ita sau uku a wannan matakin na gasar ta Kofin Zakarun Turai, tun 2005, kuma a duka ana fitar da ita ne.

Sai dai duk da wannan tarihi Wenger na ganin kungiyar tasa tana da kwarewar da za ta iya haddasa wa abokan karawar tata matsala.

Kociyan ya ce idan ka duba tarihinsu za ka ga ko da yaushe suna cikin kungiyoyi hudu na karshe a gasar, wanda wannan babban kalubale ne a wurinmu, amma za mu iya fuskantarsa.

A kaka shida a jere ana fitar da Arsenal daga gasar ta cin Kofin Zakarun Turai a wannan matakin na kungiyoyi 16.