Boksin: Mayweather ya musanta dambensa da McGregor

Floyd Mayweather (a hagu) da Conor McGregor. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Fabrairu na shekarar da ta wuce, Mayweather (na hagu), ya ce ana masa tayin mahaukatan kudade don ya dawo dambe

Zakaran damben boksin na ajin matsakaita nauyi na duniya wanda ya yi ritaya, Floyd Mayweather, ya musanta wasu rahotanni da ke cewa ya amince su dambata da zakaran damben UFC Conor McGregor.

A wani sako da Mayweather din ya sanya a shafinsa na Twiter, ya ce sam-sam babu wannan magana, tsakaninsa da wani dan damben boksin.

Ya ce idan da akwai wata magana akan damben da daga wurinsa za a ji.

Mayweather ya ce idan har McGregor yana son a yi damben, to ya umarci wakilansa su je su gana da nasa wakilan a tsayar da magana.

Shi dai Mayweather mai shekara 39, a watan Satumba na 2015, ya yi ritaya a karo na biyu, bayan ya kare kambinsa na WBC da WBA, inda ya yi nasara a dukkanin dambensa 49, ba tare da an taba doke shi ba.

Kuma wannan bajinta ta sa ya zo daidai da Rocky Marciano, wanda shi ma a tarihin dambensa ya yi nasara a dukkanin karawarsa 49.

Ba'amurke Mayweather, wanda ake ganin shi ne dan damben boksin din da ya fi bajinta a tsakanin sa'o'insa, ya sake yin ritaya a 2008, bayan dambensa 39.

A watan Janairu ne ya ce ya sanya wa McGregor dala miliyan 15 domin, dan Ireland din ya yarda su dambata.