Jose Mourinho ya shiga fargaba

Jose Mourinho cikin damuwa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Man United za ta yi wasa hudu na kofi, da suka hada da wasan karshe na kofin lig (EFL), kafin ta koma wasan Premier

Manchester United za ta shiga tsaka-mai-wuya a watan Afrilu da Mayu, idan ta ci gaba da nasara a gasar Kofin Europa, da Kofin FA, in ji kocinta Jose Mourinho.

Kocin dan Portugal na fargaba ne kan yadda wasannin kungiyar za su cakude a kusan karshen kakar da ake ciki.

United, wadda za ta karbi bakuncin Saint-Etienne a gasar Kofin Europa ranar Alhamis, za ta je gidan Blackburn a wasan zagaye na biyar na kofin FA ranar Lahadi.

Kocin ya ce su a Manchester United ba za su iya zabar wata gasa su bar wata ba.

A bana United ta yi wasa 38, da suka hada da 25 na Premier, da biyar na kofin lig na EFL, da kuma guda biyu na cin kofin FA na Ingila.

Kungiyar za ta yi wasa akalla 65 idan ta kai wasan karshe na Kofin FA da kuma na gasar Zakarun Turai ta Kofin Europa.