'Yar Nigeria Asisat Oshoala ta bar Arsenal ta koma China

Asisat Oshoala ( a hagu) a wasan Arsenal

Asalin hoton, THE FA

Bayanan hoto,

Asisat Oshoala (a hagu) ta taimaka wa Najeriya ta dauki kofin kasashen Afirka na mata a watan Disamba na 2016

'Yar wasan tawagar Najeriya ta mata Asisat Oshoala ta bar kungiyar Arsenal ta mata domin tafiya kungiyar Dalian Quanjian ta China.

'Yar wasan mai shekara 22, wadda ta ci kyautar gwarzuwar 'yar wasan Afirka ta BBC ta shekara a 2015, daga Liverpool ta koma Arsenal.

A watan Mayu na wannan shekara ta 2016, ta taimaka wa Arsenal din ta dauki kofin FA a Wembley.

Kuma a baya bayan nan ta samu kyautar gwarzuwar 'yar wasan Afirka ta shekara ta hukumar kwallon kafar Afirka.

Haka kuma ta yi wa Najeriya wasa a gasar cin Kofin Duniya ta mata ta 2015 a Canada.