Sai karshen kaka za a san makomar Wenger

Arsene Wenger cikin damuwa bayan wasan Munich

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Kashin da Arsenal ta sha a gidan Bayern MUnich ya jefa damarta ta kaiwa wasan dab da na kusa da karshe cikin rashin tabbas

A karshen kakar wasan bana ne za a iya sanin makomar Arsene Wenger a kungiyar Arsenal, amma kuma duk da haka akwai sabon kwantiragi da aka gabatar ma sa tun a baya.

Duk da irin yadda Arsenal din ta sha kashi a gidan Bayern Munich 5-1, ranar Laraba a wasan zagayen kungiyoyi 16 na cin Kofin Zakarun Turai, na karawar farko, ba alamar cewa kocin zai bar kungiyar kafin bazara.

Ana sa ran za a samu matsaya tsakanin kocin dan Faransa mai shekara 67 da kungiyar, a kan ya tsaya ko ya ci gaba da aiki.

A farkon kakar da ake ciki ne kungiyar ta gabatar wa Wenger wanda ya ke jagorantar kungiyar tun 1996, sabon kwantiragi.

To amma bisa al'adarsa sai a karshen kakar wasa yake yanke shawara, a lokacin ya iya yin nazarin yadda shekarar ta kasance, da kuma duba abin da zai iya kasancewa a gaba.

Rabon Arsenal da cin kofin Premier tun 2004, ko da yake akai akai kocin yana kai su gasar Kofin Zakarun Turai, inda suke kaiwa matakin sili-daya-kwale sau 14 a jere.

Sai dai yanzu bayan doke su 5-1 da Bayern ta yi, za a iya cewa kusan sau 7 kenan a jere kungiyar ta Jamus na fitar da Arsenal a gasar, a matakin 'yan 16, na sili-daya-kwale.

Yanayin yadda Bayern din ta doke Arsenal, da yadda a jere a jere ta sha kashi a hannun Chelsea da Watford a Premier, ya sa wasu tsoffin 'yan wasan Arsenal din, wasu ma sun da sun yi wasa a karkashin kocin, suke ganin lokacinsa ya zo karshe a kungiyar.

Bayan shekara tara ne Arsenal din ta dauki kofin FA a 2014, inda ta doke Hull City, sannan kuma ta kara daukar kofin a 2015.