Boksin: Da wuya a yi damben Carl Frampton da Santa Cruz.

Karon Leo Santa Cruz da Carl Frampton a dandalin MGM Grand Garden

Asalin hoton, Press Eye

Bayanan hoto,

Leo Santa Cruz ya yi nasara a kan Carl Frampton da yawan maki a dandalin MGM Grand Garden

Shugaban hukumar damben boksin ta duniya ta WBA, ta nuna shakku a kan yuwuwar karo na uku tsakanin Carl Frampton da Leo Santa Cruz.

Gliberto Mendoza ya ce kila hukumar ta WBA ta hada wata karawa ta dole tsakanin zakaran ajin marassa nauyi na duniya Santa Cruz din da dan kasarsa Mexico Abna Mares.

Frampton ya doke Santa Cruz a New York a watan Yuli na shekarar da ta wuce, 2016, kafin a karawarsu ta biyu a Las Vegas, Cruz din ya dau fansa, amma da yawan maki.

Mendoza ya nuna cewa Mares kila shi ne zai iya zama abokin karawar Santa Cruz na gaba.

'Yan damben biyu sun kara ne shekara biyu da ta wuce domin cin kambin ajin marassa nauyi na duniya na WBA a Los Angeles, inda Santa Cruz ya yi nasara a kan dan Mexicon da yawan maki.

Da yake magana a wani taron manema labarai a Panama, Mendoza ya ce, kila za a fitar da sanarwa nan da mako daya, idan Santa Cruz da Frampton suka kasa cimma matsaya kan damben nasu na uku.

Santa Cruz zai zaba tsakanin damben da za a tilasta masa na kare kambinsa da Mares, ko kuma ya ajiye kambin.

Kuma idan hakan ta kasance za ta iya bayar da damar karawar Frampton da zakaran duniya na kambin hukumar IBF Lee Selby.