Premier: Alkalin wasa Clattenburg ya koma Saudiyya

Clattenburg a lokacin da yake bakin aikinsa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Clattenburg zai bar aiki kafin wasannin Premier na gaba ranar 25 ga watan Fabarairu

Alkalin wasa Mark Clattenburg na gasar Premier zai bar aikinsa na Ingila domin ya koma Saudiyya a matsayin sabon shugaban alkalan wasan kasar.

Lafirin mai shekara 41 yawanci ana daukarsa a matsayin daya daga cikin kwararrun alkalan wasan kwallon kafa a duniya.

Kuma shi ne ya yi alkalancin wasan karshe na cin Kofin kasasahen Turai na 2016, da wasan karshe na Kofin Zakarun Turai da kuma wasan karshe na kofin FA na Ingila a kakar da ta wuce.

Mark Clattenburg zai maye gurbin Howard Webb ne, wanda shi ma wani tsohon babban alkalin wasan Premier ne, bayan da ya yi ritaya daga aikin shugabancin alkalan wasan na Saudiyya, kwanaki 11 da suka wuce.

Sabon aikin nasa da ya kulla kwantiragin shekara daya da zai iya sabuntawa akai akai, ya hada da horar da alkalan wasan kasar ta yadda za su kara kwarewa, sannan zai rika yin alkalancin wasannin gasar Saudiyyar.

Shi dai Mark Clattenburg alkalin wasa ne da a wani lokaci aka rika samun takun-saka da shi a wasu wasannin.

A daya daga cikinsu ne, tsohon dan wasan Chelsea kuma kyaftin din Najeriya John Mikel Obi, ya zarge shi da yi masa kalaman wariyar launin fata.

Kuma akan lamarin alkalin wasan ya ce ya yi ta tunanin barin aiki a lokacin.

Kungiyar alkalan wasan Premier ta yaba masa da cewa, gwani ne wanda ya zama abin koyi ga wadanda ke son zama alkalan wasan kwallon kafa.