Kofin Europa: Gent ta doke Tottenham 1-0

Da Jeremy Perbet yana Villarreal ne

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Jeremy Perbet ya ci wa Gent kwallonta a harin farko da suka kai

Tottenham ta gamu da cikas a gasar kofin Europa bayan da Gent ta Belgium ta ci ta daya ba ko daya a wasan farko na zagayen kungiyoyi 32.

Dan wasan Faransa Jeremy Perbet ne ya ci wa masu masaukin bakin kwallonsu a minti na 59, bayan an dawo hutun rabin lokaci.

A ranar Alhamis 23 ga watan nan na Fabrairu ne Gent, wadda take ta takwas a teburin gasar Belgium za ta je Wembley domin karo na biyu na wasan

Wannan shi ne karo na 7 a jere na wasan farko na sili-daya-kwale da ake doke Tottenham a gasar Kofin Europan, inda ta yi canjaras 3, aka doke ta a 4.

Tottenham ba ta taba cin gasar kofin Turai ba a Belgium, inda ta yi canjaras a biyu, ta yi rashin nasara a uku.

Wannan shi ne karon farko tun watan Nuwamba na 2011, da Tottenham ta sha kashi a jere a gasar Kofin Europa.

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Jeremy Perbet a lokacin da ya ke zura kwallo ragar Tottenham

Kwallo biyu kenan Perbet ya ci a wasa uku na karshe da ya yi wa Gent a gida a gasar Europa.

Yanzu Tottenham kwallo daya kawai ta ci a wasa hudu da suka yi a jere a baya bayan nan a dukkanin gasa, bayan sun ci 12 a wasa hudun da suka yi kafin hudun na yanzu.

Daga cikin wasa 8 da Tottenham ta kasa jefa kwallo a raga, hudu a gasar Kofin Zakarun Turai ne.

Kafin wasan karo na biyu ranar Alhamis a Wembley, Tottenham za ta je gidan Fulham a wasan zagaye na 5 na Kofin FA ranar Lahadi.

Yayin da ita kuwa kungiyar Gent za ta je wasan gasar Belgium, gidan Standard Liege, wadda ita ma take tsakiyar tebur.