Man Utd ta lallasa Saint-Etienne 3-0

Zlatan Ibrahimovic a lokacin da ya ci kwallon farko Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Zlatan Ibrahimovic ya ci wa Manchester United kwallo 23 a kakar bana

Manchester United ta lallasa bakinta Saint-Etienne da ci 3-0 a gasar kofin Europa a wasan farko na zagayen kungiyoyi 32, inda Zalatan Ibrahimovic ya ci kwallon duka.

Zlatan Ibrahimovic ne ya ci wa United dukkanin kwallon uku, inda ya fara daga raga a minti na 15 da wasan.

Bayan an shiga lokaci na biyu kuma na wasan ne kuma, an yi nisa da minti 75 sai ya kara ta biyu.

Sannan kuma a minti na 88 ne ya zura cikammakin kwallon, ta uku kenan da bugun fanareti.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kwallo ukun da ya ci, ya zama dan wasan da ya fi bajinta a wasan, abin da ya sa aka mallaka masa kwallon

Da wannan ruwan kwallo da Ibrahimovic ya yi wa Saint Etienne, kungiyar ta zama wadda ya fi zura kwallo a cikin ragarta a wasansa.

Wannan shi ne karo na 17 da Zlatan Ibrahimovic yake cin kwallo uku-uku a tarihin wasansa.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yayan Paul Pogba kenan Florentin Pogba ( a hagu) wanda ya buga wa Saint-Etienne kafin wasan ya zana lambar dan uwansa 6 a kansa

A karawar dan wasan da ya fi tsada a duniya Paul Pogba, ya fafata da yayansa Florentin Pogba, wanda kungiyar ta Faransa ta saye shi euro 500,000 a 2012.

Mahaifiyar 'yan uwan biyu, Yeo da kaninsu, Mathias, wanda ke bin Paul Pogba, sun halarci wasan.

A ranar Laraba mai zuwa ne Manchester United za ta je Faransa gidan Saint Etienne domin wasan karo na biyu.

Gaba daya wasanni 16 aka yi na Kofin na Europa ranar Alhamis din, daga ciki Roma ta bi Villareal ta doke ta 4-0.