Tabbas zan yi aikin koci badi ko ba a Arsenal ba — Wenger

Arsene Wenger

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kontiragin Arsene Wenger a matsayin kociyan Arsenal zai kare a karshen kakar bana

Arsene Wenger ya ce tabbas zai yi aikin koci a kakar wasan badi ko a kungiyar Arsenal ko a wata kungiyar kwallon kafar daban.

Wenger, mai shekara 67, ya yi wannan furucin ne a karshen daya daga cikin makonni mafi wahala a gare shi cikin shekara ashirin da ya yi yana jagorantar kungiyar Arsenal.

Bayan kayen da Asernal ta sha a wajen Bayern Munich 5-1 a gasar zakarun Turai, wasu tsoffin 'yan wasan Asernal din sun ce sun yi imanin cewar lokacinsa a matsayin jagoran kungiyar ya zo karshe.

Kontiragin kocin dan kasar Faransa, zai kare ne a karshen kakar bana, kuma ya ce zai yanke shawara kan wata sabuwar yarjejeniya a watan Maris ko Afrilu.

"Ko me ya faru, zan jagoranci wata kungiya tsawon kakar wasa daya daya. Ko a nan ko kuma a wani wuri na daban. Ina da tabbacin wannan," inji Wenger a ranar Juma'a.

Ya kara da cewa, "Idan na ce a watan Maris ko Afrilu, na fadi haka ne saboda ban sani ba. Ba na son in sauya hakan.

"Na saba da suka. Ina ganin a rayuwa abu mai muhimmanci ne ka yi abin da ka ke tunanin ya fi dacewa. Ina aikin da ya shafi jama'a ne, kuma dole in lamunci hakan."

Tun a shekarar 1996 ne Arsene Wenger ke jan ragamar kungiyar Arsenal.