Tanzania: An tuhumi cibiyoyin agaji da bai wa 'yan luwadi kula

Tanzaniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamnatin Tanzaniya ta ce tana son habaka ba da kulawa ga masu cutar kanjamau a kasar.

Gwamnatin Tanzania ta hana cibiyoyin lafiya masu zaman kansu 40 bayar da kulawar da ta jibinci cutar kanjamau, tana mai tuhumarsu da bai wa 'yan luwadi kula sosai.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito ministan lafiyar kasar Ummy Mwalimu, yana cewa, ya yi amanna cewar kungiyoyi masu zaman kansu suna amfani da wasu cibiyoyin lafiya na kasar domin kara bai wa masu luwadi muhimmanci.

Mista Mwalimu ya kuma sanar da cewar gwamnatin tana fadada kulawar da take bai wa masu cutar HIV/AIDS a cibiyoyin lafiya 3,000 a fadin kasar.

Ya kuma ce a watan Satumbar da ta gabata ne, gwamnatin ta dakatar da kulawar da ake bai wa masu cutar kanjamau na wucen gadi ga maza 'yan luwadi.

Luwadi babban laifi ne a kasar da zai iya kai mutum ga zaman kurku na shekara 30.