Gareth Bale zai fara buga wasa bayan warkewarsa

Gareth Bale
Bayanan hoto,

Gareth Bale ya warke daga jinya

Gareth Bale ya shirya tsaf don fara buga wasa a karon farko tun watan Nuwambar da ta gabata, bayan ya haye gwajin da aka yi masa don buga wa Real Madrid wasa ranar Asabar.

'Dan wasan mai shekara 27 ya bar buga tamaula ne tun bayan da aka yi masa aiki a gwiwa a Nuwambar 2016.

Wasa na gaba da Wales zai yi shi ne na fidda gwani a na gasar cin kofin duniya na 2018, wanda za su kara da Ireland a birnin Dublin a ranar 24 ga watan Maris.

Kocin kungiyar Madrid Zinedine Zidane ya ce, "Yana cikin tawagar kuma an shirya cewa zai yi wasa na 'yan mintina ne."

Madrid na gaban Barcelona da maki daya a gasar La Liga ta Spaniya.

"Bale dan wasa ne mai matukar muhimmanci gare mu. Kun san yadda ya kware da kuma yadda yake da hanzari," inji Zidane.

Ya kara da cewa dan wasan ya yi makukar fari cin sake dawowa fagen tamaula.