Jose Mourinho: Chelsea ta riga ta lashe gasar Premier

Jose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jose Mourinho ya ce Chelsea ta mai da hankali akan gasar kofin FA

Kocin Manchester United, Jose Mourinho, ya ce ya kamata Chelsea ta mai da hankali kan gasar kofin FA saboda ta riga ta lashe kofin gasar Premier.

Kungiyar ta Antonio Conte wacce zata dauki bakuncin United a watan Maris, tana gaban Man U da maki takwas a gasar Premier yayin da ya rage wasa 13 da za ta buga.

Chelsea ta samu zuwa mataki na gaba ne bayan ta doke Wolves 2-0 a zagaya na biyar, yayin da United ta sha Blackburn 2-1.

Tsohon kocin Chelsea, Mourinho ya ce ''Kofin FA abu ne mai muhimmanci a gare su''.

Akwai yiwuwa Chelsea zata lashe gasar Premier karo na biyu cikin shekara uku, bayan Mourinho ya ci gasar da su a kakar 2014 da na 2015.

A bayan watanni bakwai ne aka sallami dan Portugal din, a lokacin da abin da ya rage kungiyar ta fice daga gasar maki daya ne kacal.