Arsenal za ta karbi bakuncin Spur

Arsenal
Bayanan hoto,

Kungiyar mata ta Arsenal ta lashe gasar mata ta FA a karo na 14 a shekarar 2016

Kugiyar mata ta Arsenal za ta karbi bakuncin Tottenham a zagaye na biyar na Gasar Kofin FA ta mata, yayin da ake shiga matakin kungiyoyi 16.

Kungiyar Spurs, wadda daya ce cikin kungiyoyi biyun da ke kasan teburin gasar ta mata da suka rage a kakar bana, ta lallasa Brighton da ci biyu ranar Lahadi.

Akwai kuma karon battar da za a yi tsakanin Liverpool da Everton da kuma wasu wasannin biyu na rukuni na biyu na gasar mata.

An shirya buga wasannin na zagaye na biyar a ranar Lahadi, 19 ga watan Maris.

Manchester City za ta karbi bakuncin Reading, yayin da Notts County kuma za ta karbi bakuncin Yeovil a daya gasar ta rukuni na daya na gasar ta mata.