Me Ancelotti ke nufi da nuna wa 'yan kallo yatsa?

Bayern tana kan gaba da maki biyar a gasar Bundes Liga
Bayanan hoto,

Bayern tana kan gaba da maki biyar a gasar Bundes Liga

Hukumar kwallon kafar Jamus ta nemi kocin Bayern Munich Carlo Ancelotti, da yayi bayanin abin da yake nufi da nuni da dan yatsar tsakiya da yayi ga magoya bayan kungiyar Hertha Berlin a ranar Asabar.

Ancelotti ya yi nuni da dan yatsar ne a lokacin da yake tafiya a hanyar fita daga filin wasan, bayan an tashi a karawar da kungiyarsa ta yi canjaras a birnin Berlin, inda ta farke cin da Hertha Berlin ta yi mata a minti na 95 kafin tashi daga wasan.

Ya shaida wa wani dan jarida cewa yayi hakan ne saboda tofa masa yawu da aka yi.

Amma akwai yiwuwar kocin - dan Italiya, zai fuskanci hukuncin ladabtarwa, sai dai a yanzu an bukaci ya bayyana ma'anar abin da ya yi din ne a rubuce.

An kuma ba shi nan da yammacin ranar Talata ne ya yi hakan, kafin daga bisani hukumar kwallon kafar Jamus din ta shawarta abin da ya kamata ta yi.

A wata sanarwa da Bayern din ta fitar ta ce, :"Kwamitin sa ido na hukumar kwallon kafar Jamus ya yi kira ga Carlo Ancelotti da ya gabatar da bayani a rubuce kan abin da ya faru bayan karawar kungiyarsa da Hertha Berlin."

Kungiyar Bayern din ta tabbatar da cewa tabbas kocin nata zai yi abin da aka umarce shi da yi.