'Ba mu fara tunanin mai maye gurbin Enrique ba'

Magoya bayan Barcelona sun fara nuna gajiyawarsu da Enrique
Bayanan hoto,

Magoya bayan Barcelona sun fara nuna gajiyawarsu da Enrique

Kungiyar Barcelona ta ce ba ta da wani shiri na maye gurbin kocinta Luis Enrique, wanda zai san makomarsa ta aikin koci a watan Afrilu.

Kwantiragin Enrique za ta kare ne a karshen kakar wasannin bana, kuma a ranar Lahadi ne magoya bayan kungiyar suka yi masa sowa bayan da kungiyar Leganes ta lallasa su 2-1 a karawarsu.

Mamallakin kungiyar Josep Maria Bartomeu, ya ce "A son ranmu dai Enrique ya ci gaba da rike mukaminsa."

"A 'yan shekarun da suka gabata, ya lashe kusan dukkan gasar da muka yi. Magoya bayan Barca suna farin ciki da shi," a cewar Bartomeu.

Bartomeu ya kara da cewa, "Za mu tattauna da Enrique a watan Afrilu don mu ji yadda zai dauki abin. Ba mu da wani shirin wanda zai maye gurbinsa.

"Yana yin aiki tukuru kuma yanzu mun shiga mataki mafi muhimmanci a kakar wasannin."

A shekarar 2014 ne Mista Enrique, dan shekara 46, ya zama kocin Barcelona.

Ya samu nasarar cin gasar Zakarun Turai da La Liga da gasar Copa del Rey a kakar wasanni na farko da ya yi a kungiyar.

Amma wannan kakar wasan ta zo masa da matukar wahala, don a ranar Talata ma Paris St-Germain ta lallasa Barcelona da ci 4-0.