Cin hanci: Barcelona da Neymar za su fuskanci hukunci

Neymar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Neymar ya ci kwallaye 95 a wasanni 171 da ya yi wa Barca tun lokacin da ya koma can a 2013

Kungiyar Barcelona da dan wasanta na gaba Neymar za su fuskanci hukunci kan tuhumar cin hanci da ake musu na batun sayo dan wasan daga kungiyar Santos ta Brazil, bayan rashin nasarar da suka samu a daukaka karar da suka yi.

Karar ta shafi wani korafi ne da wani kamfanin saka jari na Brazil DIS, ya gabatar, wanda shi yake da kashi 40 cikin 100 na hakkin sayen dan wasan.

Kamfanin ya ce an rage kudin da aka tsara za a ba shi tun farko a lokacin da Neymar ya koma Barcelona daga Santos, a kan kudi fam miliyan 49 a shekarar 2013.

Kungiyar Santos da mahaifiyar Neymar, da wani kamfani mallakin iyayen dan wasan ma za su fuskanci hukunci.

A wata sanarwa da ta fitar, babbar kotun Spaniya ta ce, "Kungiyar Santos da kungiyar Barcelona da Neymar da mahaifiyarsa da kamfaninsu ba su yi nasara ba a karar da suka daukaka na neman a kori shari'ar da ake tuhumarsu da cin hanci."

Wannan hukunci na nuna cewa ba za su iya sake daukaka kara ba.

Masu shigar da karar suna bukatar a yanke masa hukuncin daurin shekara biyu da kuma tarar kusan fam miliyan takwas.

Suna kuma bukatar a ci tarar kungiyar Barcelona fam miliyan 7.2 da kuma fam miliyan 5.6 ga kungiyar Santos.

Barcelona ta zaci cewa an rufe zancen a lokacin da wani alkali ya rufe babin shari'ar a watan Yunin 2016, amma sai mai shigar da kara a Spaniya ya dawo da batun shari'ar a watan Satumba, inda aka ci gaba da yin ta.