Nigeria na goyon bayan abokin hamayyar Issa Hayatou

Ahmad Ahmad

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shin Ahmad Ahmad na Madagascar's Ahmad Ahmad zai kawo wani sauyi a kwallon kafar Afirka?

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya na goyon bayan kalubalantar dadadden shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka Issa Hayatou.

Mista Hayatou yana takarar wa'adi na takwas a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka, inda za su fafata da shugaban hukumar kwallon kafa ta Madagascar Ahmad Ahmad, wanda shi ma yake neman kujerarsa.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick, ya shaida wa BBC cewar zaben zai kasance wani yanayi na sauyi ga kwallon kafar Afirka.

Ya ce Ahmad ya nuna bajinta sosai wajen fitowa ya kalubalanci Mista Hayatou.

Mista Yahatou dan asalin kasar Kamaru, ya shafe shekaru da dama yana jagorantar hukumar.