An wawushe shagunan baki a Afirka ta Kudu

Afirka ta Kudu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Bakaken fata 'yan Afirka da 'yan Asiya ake nuna wa kyama a Afirka ta Kudu

Wata Jaridar Afirka ta Kudu ta ambato mai magana da yawun 'yan sanda, Bongi Msimango, yana cewa an wawushe kayayyakin shagunan kusan 30 na bakaken fata 'yan wasu kasashen da ke zama a Afirka Ta Kudu, a ranar Litinin da daddare, a Pretoria, babban birnin kasar.

Mista Msimango ya ce, "An fasa shagunan bakin ne a anguwar Atteridgeville, kuma lamarin ya kai har anguwar Lotus Gardens da ke makwabtaka. 'Yan Sanda sun samu sun shawo kan lamarin kuma ba a sake samun wani rahoto ba daga baya."

Jami'in 'yan sandan ya ce, "Wasu daga cikin masu shagunan na ciki a lokacin da abin ya faru, amma babu wanda ya ji ciwo. Ba mu san me ya sa wannan rikicin ya tashi ba."

'Yan sanda ba su san 'yan wadanne kasashe ne aka kai wa harin ba.

Amma lamarin ya faru gabannin wani macin da kungiyar mazauna Memolodi ke shirin yi ranar Juma'a, don nuna kin jinin bakin da basu da izinin zama a kasar.

A ranar Litinin ne dai gwamnatin Najeriya ta yi kira ga kungiyar Tarayyar Afirka da kuma gwamnatin Afirka ta Kudu, da su dau matakin dakile hare-hare kin jinin bakin da ake shirin yi a kasar.

Wannan ba shi ne karo na farko da ake kai wa baki bakaken fata hari ba a Afrika ta Kudu.