Ranieri : Na so barin Leicester

Claudio Ranieri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasa daya kawai aka ci Leicester a gasar cin Kofin Zakarun Turai a bana

Kocin Leicester Claudio Ranieri ya ce tun a bara, bayan da suka dauki kofin Premier ya so ya bar kungiyar, amma ya zabi ya ci gaba da zama domin ya gina wani abu kyakkyawa.

Kocin ya bayyana hakan ne yayin da kungiyar ke shirin fafatawa a gidan Sevilla a karawar farko ta Kofin Zakarun Turai na kungiyoyi 16 a ranar Laraba.

Ranieri ya ce, bayan da ya dauki kofin Premier a bara, wasu kungiyoyin sun nuna bukatarsu da shi, amma kuma yana son ya tsaya a Leicester, duk da cewa ya san shekara ce da za ta kasance mai wuya.

Ya ce duk da haka, ya ci gaba da karfafa wa kansa guiwa ya jure, ya manta da kofin, domin yana son ya samar da wani abu mai kyau ga magoya baya da shugaba kuma ita kanta kungiyar.

Ranieri ya ce wasan da za su yi da Sevilla zai iya kasancewa wanda zai kawo musu sauyin halin da suke ciki na rashin tabuka abin-a-zo-z-gani a Premier a bana.

Kocin ya ce, suna bukatar wasa irin wannan, domin idan suka yi nasara, lamarin zai iya sauyawa.

Zakarun Premier na fama a gasar a kakar nan, domin a yanzu maki daya ne da kuma mataki daya tsakaninsu da rukunin masu faduwa daga gasar.

Sai dai kuma duk da haka sun ci wasansa hudu daga cikin shida na gasar cin Kofin Zakarun Turai a bana.

Leicester wadda za ta je Sevilla ba tare da dan wasanta na gaba Islam Slimani ba saboda raunin da ya ji a matse matsi ba, tana da gagarumin aiki a gabanta a haduwar da kungiyar, da ta dauki kofin Europa sau biyar, kuma wannan shi ne karo na biyu a jere da take zuwa gasar Zakarun Turai ta Uefa.

Sevilla tana matsayi na uku a teburin La Liga, kuma sau biyu ana doke ta a gida a bana, inda Barcelona ta ci su a La Liga, sannan kuma Juventus ta ci su a gasar Zakarun Turai.