Juventus ta hukunta Bonucci

Bonucci da abokan wasansa a lokacin atisaye

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bonucci ya ce dole ne Juventus ta mutunta Porto

Dan wasan baya na Juventus Leonardo Bonucci ba zai yi wasansu na ranar Laraba, na karon farko na kungiyoyi 16 na Zakarun Turai da FC Porto ba, saboda ya yi rigima da kocinsu, in ji kungiyar.

Bonucci, mai shekara 29, ya yi sa-in-sa ne da kocinsu Massimiliano Allegri bayan wasansu na ranar Juma'a da suka ci Palermo 4-1 a gasar Serie A.

Kocin ya ce an dauki matakin ne domin kare kima da martabar kungiyar da 'yan wasanta da kuma magoya bayanta.

Haka kuma kungiyar ta ci tarar Bonucci akan rikicin da ya yi da kocin nasa.

Dan wasan ya ce ya yarda abin da ya yi bai dace ba, kuma ya bayyana cewa zai yi sadaka ga wata kungiyar agaji domin sasanto.

Haka su ma 'yan wasan kungiyar na baya Andrea Barzagli da Giorgio Chiellini ba a jin za su yi wasan na yau saboda raunin cinya, yayin da ita Porto ba ta da wani dan wasanta da ke jinya.

Juventus wadda a wasan karshe na 2015 na Kofin na Zakarun Turai aka doke ta, tana daga cikin kungiyoyin da ake sa ran za su dauki kofin a birnin Cardiff na yankin Wales a watan Mayu.

Wasan na ranar Laraba zai kasance karo na 17 da mai tsaron gida Gianluigi Buffon da Iker Casillas za su fuskanci juna.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Buffon da Casillas kowanne ya dauki kofin lig 12, da kofin duniya bibbiyu da kofin Zakarun Turai bibbiyu da kuma kofin kasashen Turai dai-dai

Hamayyar tasu ta faro ne tun kusan shekara 20 da ta wuce, kuma golan Porto Casillas, mai shekara 35,har yanzu yana matukar sha'awar Buffon mai shekara 39.

Casillas ya ce ya yi sa'a sosai bai kai shekarun Gigi, kamar yadda yake yi masa inkiya ba.

Ya ce yana dan shekara 14 lokacin da ya fara wasa, yayin da shi kuma Buffon yake 18, wanda hakan ya sa ya samu damar ganin yadda yake wasa, da kuma yadda yake.

Ya kara da cewa yayin da yake tasowa, ya rika koyi da shi, har suka cigaba tare a sana'a daya.

Golan dan Spaniya ya ce hamayyarsu mai kyau ce, ba ta gaba ba ce, domin suna matukar girmama junansu, kuma yana sha'awar karawa da shi a ko da yaushe.