Idan Rooney zai koma China ina za shi?

Wayne Rooney

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ba shakka kungiyoyin China da dama za su karbi Rooney hannu bibbiyu

Kamar yadda al'amura suke a yanzu, kusan kungiyoyi uku ne kawai suke da karfin arziki da gurbin da za su iya sayen Wayne Rooney.

A kwanan nan hukumar kwallon kafa ta China ta bullo da wata doka da ta takaita yawan 'yan wasan waje da kowace kungiya za ta iya amfani da su a wasa, zuwa uku kawai.

Bisa tsarin dokar kungiya za ta iya sayen 'yan wasan waje da ba su wuce biyar ba, wadanda suka hada da daya daga wata kasa ta nahiyar Asiya.

A dalilin haka, kungiyar Beijing Guoan da Jiangsu Suning da kuma Tianjin Quanjian su ne ga alama za su iya zawarcin Rooney, sai dai idan wasu kungiyoyin da za su so shi, sun sallami wasu 'yan wasan na waje ko kuma su tura so zaman aro.

Kocin Tianjin, Fabio Cannavaro, ya ce a kwanan nan kungiyar ta nemi dan wasan, amma kuma ya ce yana ganin dan wasan mai shekara 31 bai dace da tsarin wasan kungiyar ba.

Kungiyar Jiangsu, wadda tsohon dan wasan Chelsea na tsakiya Ramires ya koma, tana daga cikin zabin da Rooneyn zai iya komawa.

Amma kuma wadda dai ake ganin za ta fi dacewa da shi, ita ce Beijing Guoan.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kungiyar na daya daga cikin tsoffin kungiyoyin kwallon kafa a China, kuma ana rade radin cewa tana samun goyon bayan Shugaba Xi, wanda ke fatan ganin ya sa kasar ta zama gagaruma a duniya a fagen wasannin.

Beijing da Shanghai, su ne manyan biranen da suke da tsarin rayuwa da 'yan kasashen waje sosai a kasar ta China, wadanda inda dan wasan na Manchester United da Ingila zai koma can, zai samu tsarin rayuwa da irin makarantun da za su dace da 'ya'yansa da matsara Coleen.

Akwai tarnaki da dama a kan tafiyar dan wasan mai shekara 31 zuwa China, wadanda wasu sun wuce ikon dadadden wakilinsa Paul Stretford.

A watan Janairu hukumomin kasar ta China suka kawo wani tsari mai tanade-tanade 18 domin takaita abin da suka ce dakatar da kashe makudan kudade a kan 'yan wasa 'yan kasashen waje.

Sir Alex Ferguson shi ne ya yanke hukunci kan tafiyar Rooney Manchester United daga Everton.

A wannan karon kuwa ana ganin tafiyar tasa za ta bukaci amincewar shugaban kasar China da kansa.

To kan maganar kudi kuma fa?

A yanzu Rooney yana samun fam dubu 300, a duk mako, kusan fam miliyan 15.6 a shekara, kafin haraji.

Ganin cewa abu ne mai wuya Manchester United ta sabunta kwantiraginsa bayan shekara 13 a kungiyar, da wuya a ce ya bar wata damar tafiya China, idan aka yi la'akari da dimbin kudin da zai iya samu a can.

Rahotanni sun ce wakilan dan wasan sun yi magana da kungiyar Tianjin Quanjian, amma kocinta Fabio Cannavaro ya ce ba wani cigaba da aka samu.

Ana ganin da wuya a cimma matsaya kan cinikin nan da mako mai zuwa, wanda hakan ya sa ake ganin Rooneyn zai ci gaba da zama a United har zuwa karshen kakar nan.

Idan so samu ne an fahinci cewa Rooney ya fi son zama a Man United har zuwa karshen kwantiraginsa, wadda za ta kare a 2019, amma rashin sanya shi a wasa, ya sa yake sauya tunani a kai.

Kocinsu Jose Mourinho ya ki ya bayar da tabbacin ko kyaftin din na Ingila zai ci gaba da zama a kungiyar har bayan lokacin da kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta China za ta rufe 28 ga watan Fabrairu.

Rooney ne dan wasan da ya fi ci wa United kwallo a tarihi, kuma ya dauki kofin Premier biyar da tun lokacin da ya koma kungiyar yana dan shekara 18.

A ranar Larabar nan ne Saint-Etienne za ta karbi bakuncin Manchester United a karo na biyu na wasansu na zagayen kungiyoyi 32 na kofin Turai na Europa.