Liverpool za ta gina sabon filin atisaye

Filin atisayen Liverpool

Asalin hoton, LiverPool FC

Bayanan hoto,

A yanzu aikin na matakin tuntuba ne

Liverpool za ta sauya filin atisayenta a wani shiri da za ta kashe fam miliyan 50 domin fadada cibiyar renon matasan 'yan wasanta.

Kungiyar ta Premier tana shirin sayar da filin atisayenta na Melwood da ke West Derby, inda 'yan wasanta na farko suka fara yin atisaye tun shekarun 1950.

Aikin wanda zai gudana bisa hadin guiwa tsakanin kungiyar ta Liverpool da karamar hukumar Knowsley zai sa ta koma da cibiyar atisayen nata zuwa yankin Kirkby.

Idan har aka amince da shirin to ana sa ran za a iya kammala shi zuwa shekara ta 2019.

Babban jami'in kungiyar, Andy Hughes,ya ce hada tawagar manyan 'yan wasan kungiyar da matasanta wuri daya abu ne da zai yi kyau sosai.

Ya ce sabbin abubuwa na zamani da za a sa a sabon filin wasan, za su taimaka wajen horar da 'yan wasan da kyau, kuma tsarin da za a yi na rufe filin, zai sa a yi yadda zai rika dacewa da atisayen kowane irin yanayi.

Liverpool na bukatar sayen karin fili a yankin na idan har za ta aiwatar da wannan aiki, wanda zai sa ta sayar da waccan cibiyar ta Melwood, wadda take ganin za a iya sauya ta a gina gidaje 160.

Tsohon kocin Liverpool Gerard Houllier shi ne ya shugabanci babban aikin sake fasalin filin atisayen kungiyar na Melwood a shekarar 2001, inda ya zamanantar da filin ya kasance daya daga cikin mafiya kyau da kayawatarwa a duniya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A Melwood jama'a kan je leken atisayen 'yan wasan na Liverpool

Sai dai matsalar killace 'yan wasa ce ta zama abin damuwa ga kungiyar a Melwood, inda mutane suke amfani da tsani da kujeru, suna leken kallon 'yan wasan a lokacin atisaye.