Europa: Man Untd ta je matakin 'yan 16

Henrikh Mkhitaryan a lokacin da ya ci Saint-Etienne
Bayanan hoto,

Bayan da Henrikh Mkhitaryan ya ci kwallo daya tilo ta wasan ya fita, bayan minti tara saboda raunin da ya ji a cinya

Manchester United ta yi nasarar zuwa matakin gaba na kungiyoyi 16, na cin kofin Turai na Europa bayan da ta bi Saint-Etienne ta Faransa har gida ta sake

A makon da ya wuce ne Manchester United ta doke kungiyar ta Faransa da ci 3-0 a Old Trafford.

Bayan minti 16 da fara wasan ne sai Mkhitaryan ya daga ragar Saint-Etienne.

Kwallon daya tilon da Mkhitaryan ya ci wa United a karawar ta ranar Laraba, ta sa kungiyar Manchestern ta tsira da kwallo 4-0 kenan jumulla wasa gida da waje.

Sai dai ana ganin Manchester United ta gamu da matsala domin bayan da Mkhitaryan ya ci kwallon, ya fice daga wasan bayan minti tara saboda ya ji rauni a cinyarsa.

Kuma a sanadiyyar hakan kila dan wasan dan Armenia, ba zai yi mata wasan karshe da za ta yi da Southampton ba na kofin kalubale na Lig (EFL), wanda za su yi ranar Lahadi, 26 ga watan Fabrairu, a Wembley, da karfe 05:30 na yamma agogon Najeriya.

Sai dai Jose Mourinho na ganin dan wasan zai iya samun saukin raunin kafin karawar.

A sauran wasannin da aka yi ranar Larabar, Fenerbahce a gidanta ta yi kunnen doki da 1 - 1 da Krasnodar, abin da ya ba wa Krasnodar nasarar tsallakewa zuwa matakin 'yan 16 da ci 2-1 jumulla.

Ita kuwa Schalke 04 ta yi kunnen doki 1-1 ne a wasansu, abin da ya sa ta yi waje da POAK da ci 4-1, ta tsallake zuwa matakin kungiyoyi 16 na kofin na Europa.

A ranar Alhamis 23 ga watan Fabrairu, za a yi sauran wasanni 13 na zagayen kungiyoyi 32, domin tace sauran cikammakin 16, da za a fitar da jadawalin haduwarsu a cikin makon nan.

Daga cikin wasannin Tottenham za ta karbi bakuncin Gent, wadda a makon da ya wuce ta ci kungiyar ta Premier 1-0.

Roma wadda ta bi Villareal gida ta ci ta 4-0 a makon da ya wuce, a ranar Alhamis din za ta karbi bakuncin kungiyar ta Spaniya.