Valencia ta shammaci Real Madrid 2-1

'Yan Valenci na murnar kwallon da suka ci

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Sau uku Valencia na sake koci a bana

Real Madrid ta sha kashi a karo a biyu a gasar La Liga a bana, inda Valencia a gidanta ta shammace ta da ci 2-1.

Tsohon dan wasan gaba na West Ham Simone Zaza ne ya fara ci wa masu masaukin bakin kwallo minti 4 da shiga fili, sannan kuma minti 5 tsakani sai Fabian Orellana ya kara ta biyu.

Ana dab da shirin tafiya hutun rabin lokaci ne a minti na 44 sai Cristiano Ronaldo wanda ya yi wasansa na 700 a kungiya ya farke daya.

Maki daya ne tsakanin Real Madrid ta daya a tebur, wadda kuma take da kwantan wasa daya, da Barcelona ta biyu mai maki 51.

Zaza, mai shekara 25, dan Italiya sau 11 yana wasa amma bai ci wa Valencia ba, kuma a karshen mako ne ya fashe da kukan murna bayan da ya ci kwallonsa ta farko tun watan Mayu.

Nasarar ta sa Valencia wadda Voro ya kasance kocinta na uku a bana ta yo sama a tebur zuwa ta 14 da maki 26 a wasa 23.