Kofin Duniya: Afirka na neman gurbi 10

Kyaftin din Nigeria Joseph Yobo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Nigeria da Algeria su ne kasashen Afirka da suka fi kwazo a gasar Kofin Duniya ta 2014, inda sukla je zagayen 'yan 16

Africa za ta nemi a linka mata yawan gurbin da ake ba ta a gasar cin Kofin Duniya daga biyar zuwa 10 a gasar da za a kara yawan kasashe ta 2026.

Shugabannin hukumomin kwallon kafa na nahiyar, sun sheda wa Fifa, cewa suna son akalla gurbi 10 a gasar da za a yi mai kasashe 48.

Dukkanin hukumomin kwallon kafa na duniya sun goyi bayan tsarin Fifa, na kara yawan kasashen, kuma Afirka na sa ran samun gurbi 10 , in ji shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu Danny Jordaan.

Hakan na nufin Afirka za ta samu linki biyu na gurbin da take da shi a gasar cin Kofin Duniya da za a yi a 2018 da 2022.

Nahiyar Turai na neman akalla gurbi 16 daga 3, kuma tana son a rarraba kasashen nata, ta yadda ba za su hadu a rukuni daya ba, inda wata za ta yi waje da wata ba.

Nahiyar Asiya na sa ran samun gurbi 8 zuwa 9, sabanin hudu da rabi da ake ba ta a yanzu, yayin da Latin Amurka ke neman 10, karin shida daga hudu da rabi da ake ba ta.

Yankin Caribbean da tsakiya da Arewacin Amurka za su samu gurbi shida da rabi, sabanin uku da rabin da ake ba su, inda dan karamin tsibirin Pacific na Oceania zai samu gubi daya kai tsaye mai makon rabi da akae ba shi a da.

Duka wannan dai taron majalisar Fifa ne zai amince kafin ya tabbata.