Zakarun Turai: Leicester ta nuna jarunta

Jamie Vardy a lokacin da ya jefa kwallo ragar Sevilla

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Ranieri na fatan kwallon da Vardy ya ci za ta kawo karshen kamfar zura kwallonsa a bana

Kocin Leicester Claudio Ranieri ya yaba wa kungiyarsa kan yadda ya ce ta nuna jarunta, bayan da Jamie Vardy ya ci musu kwallo daya a gidan Sevilla wadda ta doke su 2-1 a wasan Zakarun Turai na matakin kungiyoyi 16, karon farko.

An zura wa kungiyar kwallo biyu ba ko daya kafin Vardy ya ci kwallon, a wasn na ranar Laraba, a karon farko tun ranar 10 ga watan Disamba.

Leicester za ta karbi bakuncin Sevilla a wasan nasu na biyu ranar 14 ga watan Maris, a filin wasanta na King Power Stadium.

A wata hira da ya yi da BBC Ranieri ya ce, sun nuna kwazo da juriya, kuma daman idan suna irin wannan karawa, sa'a tana zuwa garesu. Kuma ya kara da cewa dole ne su kara jajircewa.

Daman kafin wasan na ranar Laraba, kocin ya ce wasan zai iya kasancewa wanda zai sauya musu al'amura, kan halin da suke ciki na neman faduwa daga gasar Premier, inda maki daya ne da mataki daya kuma ke tsakaninsu da rukunin masu faduwa daga gasar.

Kwallon da Vardy ya ci a wasan ta kawo karshen kamfar zura kwallon da yake yi a wasa tara, kuma kocin nasu na ganin, za ta ba wa dan wasan na Ingila da sauran 'yan kungiyar ta Leicester karfin guiwa, a sauran wasanninsu na bana.

Leicester za ta karbi bakuncin Liverpool ne a wasanta na gaba na Premier a ranar Litinin 27 ga watan Fabrairun nan.