Santi Cazorla ba zai kara wasa ba bana

Santi Cazorla

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Cazorla ya koma Arsenal ne daga Malaga a kan fan miliyan 15 a shekarar 2012

Dan wasan tsakiya na kungiyar Arsenal Santi Cazorla ba zai sake wasa ba a kakar nan, saboda raunin da ya ji a kafa.

Rabon Cazorla da wasa tun lokacin da ya fice daga fili yana dingishi a wasansu na cin Kofin Zakarun Turai na matakin rukuni, wanda suka yi da Ludogorets a Emirates a watan Oktoba.

A watan Disamba ne aka yi wa dan wasan mai shekara 32 aiki a asibiti, kuma tun daga lokacin kocinsu Arsene Wenger yake fatan zai warke ya dawo wasa kafin karshen kaka.

To amma yanzu Cazorla wanda ke yi wa tawagar kasarsa Spaniya wasa, ya mayar da hankalinsa ne kan murmurewa daga jinyar, yadda zai fuskanci kaka mai zuwa.